Ministan Tsaro Badaru Abubakar Ya Ajiye Aikin sa
Ministan tsaron Najeriya, Alhaji Mohammed Badaru Abubakar, ya ajiye aikin sa nan take.
A wata takarda da ya aikawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu, dauke da kwanan watan 1 ga Disamba, ta nuna cewa Badaru ya yi murabus ɗin saboda dalilai na lafiya.
Shugaba Tinubu ya amince da murabus ɗin, tare da gode masa bisa hidimar da ya bayar ga ƙasa.
An yi tsammanin Shugaba Tinubu zai tura sunan wanda zai maye gurbin Badaru zuwa Majalisar Dattawa cikin wannan makon.
Mohammed Badaru Abubakar, mai shekaru 63, ya taɓa zama gwamnan jihar Jigawa na tsawon wa’adi biyu (2015–2023), kafin a naɗa shi a matsayin minista a ranar 21 ga Agusta, 2023.
Murabus ɗin sa na zuwa ne a daidai lokacin da Shugaba Tinubu ya ayyana dokar ta ɓaci kan harkokin tsaro a faɗin ƙasar, inda ake jiran karin bayani kan matakan da za a ɗauka.


