Kwankwaso da Abdullahi Abbas sun haɗu a waje ɗaya

0
13

Tsohon Gwamnan Kano kuma dan takarar shugaban kasa na NNPP a 2023, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya haɗu da Shugaban jam’iyyar APC na Kano, Alhaji Abdullahi Abbas, a filin jirgin sama na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja ranar Juma’a.

Haɗuwar ta zo a matsayin abin mamaki ga masu bibiyar siyasa, la’akari da cewa Abbas ya dade yana sukar Kwankwaso duk da cewa ya taba zama Kwamishinan Muhalli a gwamnatinsa.

Tsohon shugaban karamar hukumar Kano Municipal, Alhaji Faizu Alfindiki, shima ya kasance tare da Abdullahi Abbas.

Wannan gamuwa ta zo kwanaki kadan bayan Kwankwaso ya yi irin ta da tsohon Shugaban APC na kasa, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, a gidan tsohon Gwamnan Bauchi, Alhaji Ahmed Mu’azu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here