Ƙungiyar AES ta kama sojojin Najeriya bayan daƙile yunkurin juyin mulki a Benin

0
12

Aƙalla sojojin Najeriya 11 ne ƙasar Burkina Faso ta tsare bayan rikicin da ya biyo bayan dakile yunkurin juyin mulki a Jamhuriyar Benin.

Kasashen Niger, Mali da Burkina Faso waɗanda suka fice daga ECOWAS bayan juyin mulki sun kafa sabuwar ƙungiya ta AES domin kalubalantar ƙungiyar ta Yammacin Afirka.

Rahotanni sun nuna cewa Najeriya ta taka muhimmiyar rawa wajen dakile yunƙurin kifar da gwamnati a Benin kafin ECOWAS ta tura dakarun ta na musamman.

Sai dai a ranar Litinin, AES ta bayyana cewa wani jirgin saman rundunar sojin Najeriya mai ɗauke da sojoji 11 ya shiga sararin samaniyar Burkina Faso ba tare da izini ba, lamarin da ya tilasta masa yin saukar gaggawa a garin Bobo Dioulasso.

AES ta ce bincike ya nuna jirgin bai samu sahalewar shiga yankin kasarta ba, tana mai kiran hakan take hakkin ƙasa da karya ƙa’idojin zirga-zirgar jiragen sama na ƙasa da ƙasa.

Kungiyar ta ce za ta harba duk wani jirgi da zai sake shiga sararin samaniyar ta ba tare da izini ba.

Har yanzu gwamnatin Najeriya ba ta fitar da wata sanarwa kan wannan mataki da AES ta dauka ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here