Kotu ta ƙi amincewa a ɗauke Nnamdi Kanu daga Sokoto

0
10

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amincewa da buƙatar da jagoran IPOB, Mazi Nnamdi Kanu, ya shigar ta neman a mayar da shi daga wani gidan gyaran tare da ɗauke shi daga jihar Sokoto zuwa wani wuri daban.

A zaman kotun na ranar Litinin, mai shari’a James Omotosho ya ce ba za a iya yanke hukunci kan irin wannan buƙata ta gaggawa ba, domin dole ne a sanar da gwamnatin tarayya wacce aka saka a cikin ƙarar domin ta bayyana matsayin ta.

Kanu, wanda aka yanke wa hukuncin ɗaurin rai-da-rai a ranar 20 ga Nuwamba kan tuhumar ta’addanci, ya riga ya daukaka ƙara kan hukuncin.

Lauyan sa Demdoo Asan, ya shaida wa kotu cewa buƙatar ta shafi gwamnatin tarayya da Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali. 

Bayan wasu tambayoyi daga mai shari’a, lauyan ya amince cewa ya dace a sanar da gwamnatin tarayya kafin a yanke hukunci.

Kotun ta daga sauraron ƙarar zuwa 27 ga Janairu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here