Wani rahoto ya nuna cewa wasu kasashe guda goma a nahiyar Afrika sun fi samun aminci da tsayayyiyar wutar lantarki, sakamakon zuba jari a harkar makamashi, fadada hanyoyin samar da wuta da kuma tsare-tsaren gwamnati da suka mayar da hankali kan haɗa jama’a da layin wuta.
A jerin, ƙasashen da suka fi samun wuta ba tare da tangarda ba sun hada da:
1. Masar
Masar tana saman jerin bayan ta cimma kusan kashi 100% na samar da wuta ga dukkan al’ummar ta, ta hanyar haɗa makamashi daga ruwa, iskar gas da sauran su.
2. Morocco
Morocco ma ta kai cikakken kashi 100% na wutar lantarki, ta dogara sosai ga makamashin rana da iska a sabon tsarin canjin ta zuwa sabbin makamashi.
3. Tunisia
Tunisia ta kai matakin 100% na samun wuta, tana amfani da gas da wasu sabbin hanyoyin samar da makamashi.
4. Algeria
Algeria na da kusan kashi 99.8% na samun wuta, a kan tsarin da ya dogara da iskar gas da kuma ci gaba da gyare-gyaren layukan sadarwa.
5. Gabon
Gabon ta kai kashi 91.6%, inda kusan duka biranen ƙasar ke da wuta, sai dai yankunan karkara na ci gaba da fuskantar kalubale.
6. Ghana
Ghana na da sama da kashi 85.9% na samun wuta, tare da dogaro ga ruwa, gas da sauran hanyoyin samar da wuta.
7. Afirka ta Kudu
Afirka ta Kudu na da kashi 84.4% na samun wutar lantarki, tana ci gaba da saka hannun jari a sabbin hanyoyin samun makamashi.
8. Botswana
Botswana ta kai kashi 72%, inda wutar birane ta fi samun ci gaba fiye da karkara.
9. Kenya
Kenya na da kimanin kashi 71%, na samun lantarki daga ruwa, iska da hasken rana.
10. Senegal
Senegal na da kusan kashi 70% na samun wuta, sannan tana fadada hanyoyin samar da wuta ta hanyar sabbin makamashi da inganta layin sadarwa.
Rahoton ya ce wadannan kasashe sun yi fice wajen aiwatar da tsare-tsaren da suka mayar da hankali kan samar da wuta ga al’umma da dorewa a bangaren makamashi.


