Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanar da komawar sa Jam’iyyar Accord, inda ya ce a karkashin jam’iyyar zai tsaya takarar wa’adi na biyu a zaben shekara ta 2026.
Adeleke ya bayyana haka ne yayin wani taron masu ruwa da tsaki da aka gudanar a fadar gwamnatin jihar, inda ya tarbi manyan jagororin jam’iyyar daga matakin jiha da na ƙasa.
Ya bayyana cewa tun ranar 6 ga Nuwamba ya yanke shawarar sauya sheka zuwa Accord, bayan tattaunawa da ya yi da shugabanni da ‘yan siyasa da kuma al’ummar jihar sa.
A cewar sa, ya zaɓi Accord ne saboda manufofin ta na tallafawa al’umma, wanda ya ce ya yi daidai da tsarin gwamnatin sa na bawa ma’aikata da jama’a muhimmanci.


