Rundunar Sojin Najeriya ta dakatar da dukkan wani nau’in ritaya ga wasu manyan hafsoshi bayan Shugaba Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan tsaro.
Wata takarda da Rundunar ta fitar ta ce an dauki matakin ne domin a ci gaba da amfani da ƙwararrun hafsoshi yayin da ake faɗaɗa yawan dakarun saboda rashin tsaron da ya ta’azzara.
Dakatarwar ta shafi waɗanda suka kure a shekarun aiki.
Rahotanni sun ce hafsoshin da ba sa son karin wa’adin za su iya yin ritaya kamar yadda aka saba, amma wadanda suka ci gaba da aiki ba za su sake samun karin girma ko wasu manyan damar ci gaban aiki ba.
Rundunar ta ce matakin na ɗan lokaci ne kuma za a sake duba shi idan tsaro ya inganta.


