Najeriya Ta Tura Jiragen Yaki Zuwa Jamhuriyar Benin Bayan Rikicin Juyin Mulki

0
10

Najeriya Ta Tura Jiragen Yaki Zuwa Jamhuriyar Benin Bayan Rikicin Juyin Mulki

Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun tabbatar da cewa rundunar sojin Najeriya ta tura jiragen yaki zuwa Jamhuriyar Benin, bayan bayyanar labarin kifar da gwamnatin Shugaba Patrice Talon da wasu sojoji suka yi a ranar Lahadi, kamar yadda jaridar Vanguard, ta rawaito.

Jiragen, waɗanda suka tashi daga Legas, an hange su a cikin sararin samaniyar Benin yayin da Najeriya ke kara sa ido kan yanayin siyasa da tsaro da ke sauyawa a ƙasar.

Wani jami’in tsaro ya bayyana cewa wannan mataki na Najeriya ba hari ba ne, illa dai bincike da tantance barazanar tsaro da ka iya tasowa ga yankin.

 “Mun tura jiragen don samar da muhimman bayanan tsaro. Muna lura da duk wani abu da ka iya tasiri ga Najeriya,” in ji majiyar.

Rahotanni sun ce sojojin da suka yi juyin mulkin a Benin ƙarƙashin jagorancin Laftanar Pascal Tigri sun ayyana rushe majalisu da sauran hukumomin gwamnati, tare da dakatar da kundin tsarin mulki na 2025. Haka kuma, an rufe iyakokin ƙasar ta ƙasa, ruwa da sararin samaniya.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here