Faransa zata taimakawa Najeriya kan matsalolin tsaro a Arewa

0
8

Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya tabbatar da kudirin ƙasar sa na mara wa Najeriya baya wajen yaki da matsalolin tsaro, musamman a yankin arewa.

A cikin sakon da ya wallafa a dandalin X, Macron ya bayyana cewa ya tattauna da Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, inda ya bayyana goyon bayan Faransa tare da neman ƙasashe abokan hulɗar su su ƙara ɗaura damara wajen tallafa wa Najeriya.

Macron ya ce: “Na tabbatar wa Shugaba Tinubu cewa Faransa na tare da Najeriya wajen fuskantar ƙalubalen tsaro, musamman a arewacin ƙasar. Idan an buƙata, za mu faɗaɗa haɗin gwiwa da hukumomin tsaro tare da tallafa wa al’ummomin da ke fama da rikice-rikice. 

Wannan bayani na Macron ya zo ne a daidai lokacin da Shugaban Amurka, Donald Trump, ke tuhumar gwamnatin Najeriya da yin sakaci wajen dakile hare-haren ‘yan bindiga kan mabiya addinin Kirista, zargin da gwamnatin Tinubu ta musanta.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here