An Kaddamar da Fom ɗin Neman Shiga Sabuwar Kungiyar Hisbar Ganduje

0
8

An kaddamar da fom ɗin neman shiga sabuwar kungiyar Hisbah ta Gandujiyya a ranar Asabar, 6 ga Disamba 2025, a jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin jigon jam’iyyar APC, Hon. Baffa Babba Dan Agundi, tare da tsohon Kwamandan Hisbah na jihar, Sheikh Harun Ibn Sina.

Majiyar Arewa Updates ta tabbatar cewa, yayin taron ƙaddamarwar, shugabannin Hisbah ta na Gandujiyya sun bayyana cewa suna shirin fito da sabbin tsare-tsare da manufofi da za su kawo sauyi tare da amfani ga al’ummar Kano.

A cewar su, wannan sabon tsarin ya haɗa da hanyoyin ba da damar sake tallafawa kusan mutane 12,000 da ake zargin an sallame su daga Hisbah ta gwamnatin jihar a baya.

An ce kwamandoji da jami’an Hisbah na bangaren Ganduje, daga kananan hukumomi 44 a fadin jihar Kano sun halarci taron ƙaddamarwar domin nuna goyon bayansu ga sabon tsarin.

Taron ya bar tambayoyi daga jama’a kan rawar da wannan sabuwar Hisbah za ta taka a tsarin tsaro da ladabtarwa, musamman kasancewar akwai hukumar Hisbah ta gwamnati mai aiki a halin yanzu.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here