Tinubu Ya Nada Christopher Musa a Matsayin Ministan Tsaro

0
5

Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya mika sunan tsohon Babban Hafsan Tsaro na ƙasa, Janar Christopher Gwabin Musa (Rtd), domin ya zama sabon Ministan Tsaro na Najeriya.

Nadin ya biyo bayan murabus da Alhaji Mohammed Badaru Abubakar ya yi a ranar Litinin sakamakon dalilan lafiya. A wasikar da Shugaba Tinubu ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya bayyana cewa Janar Musa shi ne zai maye gurbin Badaru.

Majalisar Dattawa na jiran gabatar da tantancewa kafin tabbatar da shi a hukumance.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here