Majalisar Wakilai ta Amurka ta sanar da shirin ta na gudanar da wani muhimmin taron hadin gwiwa a ranar Talata, domin nazarin rahotannin da ke cewa ana azabtar da Kiristoci a Najeriya.
Sanarwar taron ta fito ne daga ɗan majalisar Amurka, Riley Moore, wanda ya bayyana a shafin sa cewa Mataimakin Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Wakilai kuma shugaban Kwamitin Tsaron Kasa, Mario Díaz-Balart, shi ne zai jagoranci zaman.
An bayyana cewa wasu mambobin Kwamitin Kasafin Kudi da na Harkokin Waje za su taka rawar gani a tattaunawar.
Manufar zaman ita ce tattara hujjoji domin fitar da cikakken rahoto game da kashe-kashen da ake zargin suna afkawa Kiristoci a Najeriya, tare da duba irin matakan da majalisar Amurka za ta ɗauka don taimakawa wajen magance wannan matsala.
Taron na gudana ne a lokacin da ake ci gaba da muhawara tsakanin Amurka da Najeriya kan batun tsaro, sakamakon yawaitar hare-haren ‘yan bindiga da kuma yunƙurin ƙarfafa haɗin gwiwar tsaro tsakanin kasashen biyu.


