Gwamnatin Jihar Nasarawa ta sanar da cewa tana da cikakken shiri na kafa rundunar ‘yan sandan jiha idan kundin tsarin mulki ya ba da damar yin hakan.
Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar, Usman Baba, ya bayyana haka yayin ganawa da manema labarai a Lafia.
Ya ce tun farkon gwamnatin Gwamna Abdullahi Sule a 2019, an ɗauki tsaro a matsayin babban ginshiki, tare da bai wa jami’an tsaro ababen hawa, na’urori da sauran kayan aiki don ƙara inganta ayyukan su.
Ya bayyana cewa gwamnati na ƙoƙari wajen tabbatar da cewa Nasarawa ta kasance jiha mai aminci ga masu zuba jari da kuma al’umma gaba ɗaya.
Saboda haka ne aka tura jami’an tsaro zuwa makarantu da wuraren ibada, musamman a yankunan da ake nuna damuwa game da tsaro, a dukkan ƙananan hukumomi 13.
Game da matsalar garkuwa da mutane, kwamishinan ya ce ana aiki kafada da kafada da jami’an tsaro, ‘yan sa kai da masu sa ido a unguwanni domin dakile lamarin gaba ɗaya.
Ya yi gargaɗi ga masu aikata laifi cewa Nasarawa ba za ta zama mafakar su ba, inda ya ce duk wanda aka kama zai fuskanci hukunci mai tsauri.


