Gwamna Ademola Adeleke Ya Fice Daga Jam’iyyar PDP

0
8

Gwamnan Jihar Osun, Ademola Adeleke, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar PDP sakamakon rikicin da ya kunno kai a cikin shugabancin jam’iyyar a matakin ƙasa.

A cikin wata wasiƙa da ya aika wa shugaban mazaɓar sa ta Sagba Abogunde a Ede North, mai ɗauke da ranar 4 ga Nuwamba, Adeleke ya ce matsalolin da suka dabaibaye shugabancin PDP ne suka tilasta masa ɗaukar wannan mataki.

Adeleke ya gode wa jam’iyyar kan damar da ta ba shi har ya samu takara ya kuma yi nasarar zama sanata da gwamnan Jihar Osun, amma bai bayyana jam’iyyar da zai koma ba.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here