’Yan sanda sun tabbatar da sace ɗalibai mata 25 a Jihar Kebbi

0
32

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kebbi ta tabbatar da cewa ’yan bindiga sun sace ɗalibai mata 25 daga Makarantar Sakandaren ’Yan Mata ta Gwamnati da ke Maga, a Ƙaramar Hukumar Danko/Wasagu.

Lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 4 na daren Litinin, lokacin da maharan suka mamaye makarantar, inda suka kashe ma’aikaci ɗaya tare da jikkata wani. A yayin harin, an ce ’yan sanda sun yi musayar wuta da maharan, amma duk da haka suka kutsa cikin makarantar suka kwashe ɗaliban daga dakunan kwanan su.

Kakakin rundunar, CSP Nafi’u Abubakar Kotarkoshi, ya ce maharan dauke da makamai sun shigo makarantar ta hanyar haura katanga, suka kuma yi awon gaba da ɗaliban. Ya tabbatar da mutuwar mataimakin shugaban makarantar, Hassan Makuku, yayin da Ali Shehu ya samu rauni a hannunsa.

Bayan faruwar lamarin, Kwamishinan ’Yan Sanda Bello Muhammad Sani ya tura ƙarin jami’an ’yan sanda, sojoji da ’yan bijilanti domin bincike da aikin ceto. Rundunar ta ce bincike na ci gaba a yankunan da ake zargin maharan sun bi.

Kwamishinan ya roki mazauna yankin da su kasance masu kwantar da hankali, yana mai tabbatar da cewa jami’an tsaro na aiki tukuru domin kare rayuka da dukiyoyi a fadin jihar.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here