Rundunar Hisbah ta daƙile yunkurin safarar wasu ƴan mata biyu daga Kano zuwa Lagos, sannan ta kai su wasu ƙasashen Zahra’u Audu, yar kimanin shekaru 16, yar asalin Zariya dake jihar Kaduna, da Kalzihar Salim, mai kimanin shekaru 18, yar asalin ƙaramar hukumar Fagge a jihar Kano.
Mataimakin babban kwamandan rundunar Dr. Mujahideen Aminuddeen, ne ya sanar da hakan cikin wani sakon murya da aka aikowa Daily News 24 Hausa, yana mai jan hankalin al’umma ku rika kiyaye nauyin kula da tarbiyyar da Allah ya ɗora musu.
Dr. Mujahideen, yace yana da a riƙa sanya idanu a kan yara don hana su afkawa hannun masu safarar mutane da a wasu lokutan hakan ke janyo asarar rayuka ko shigar da mata harkokin karuwanci.


