Wasu ƴan Najeriya sun shiga hannu a ƙasar Kenya sakamakon aikata damfara

0
13

Hukumar Binciken Laifuka ta Kenya (DCI) ta kama wasu ƴan Najeriya uku a gidajen Mwaliko da ke garin Mwea bisa zargin gudanar da damfara ta intanet. 

An kama su ne bayan mazauna wurin sun kai ƙorafi kan halayyarsu da ke tayar da hankali, musamman da daddare.

Rahotonni sun nuna cewa mutanen sune Peter Chukwujekwu, Alazor Chukulute Sunday, da Nnalue Chiagozie Samwe, suna zaune a Kenya ba tare da takardun izinin zama ko aiki ba, duk da ikirarin cewa suna yin kasuwanci ta yanar gizo.

DCI ta ce kamun na cikin wani farmaki na haɗin gwiwa da nufin dakile ƙungiyoyin damfara a yankin. Wannan na cikin jerin kame-kamen da ake yi a ƙasashen waje kan laifukan da ake zargin wasu ’yan Najeriya, ciki har da damfara, safarar miyagun ƙwayoyi da mutane.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here