Tsohon Gwamnan Anambra, Willie Obiano, Ya Mutu a Landan

0
7

Tsohon Gwamnan Jihar Anambra, Willie Obiano, ya rasu a birnin Landan na ƙasar Birtaniya.

Majiyoyi daga danginsa sun bayyana cewa Obiano ya yi fama da matsanancin ciwon zuciya da kuma cutar sankarar mafitsara kafin rasuwarsa.

Wani É—an uwan sa ya ce: “Yayi fama da rashin lafiya mai tsawo. 

Likitoci a Landan sun tabbatar da cewa ana kula da marigayin a sashen jinya ta musamman kafin yanayinsa ya ƙara tabarbarewa.

Kafin rasuwarsa, Obiano na fuskantar shari’a a Babbar Kotun Tarayya dake Abuja kan zargin almundahanar Naira biliyan 4 daga kuɗaɗen jihar lokacin da yake mulki. An mayar da shari’ar zuwa kotun mai sharia Mohammed Umar, wadda aka tsara ci gaba da sauraren ta a ranar 25 ga Nuwamba.

Willie Obiano ya jagoranci Jihar Anambra daga Maris 2014 zuwa Maris 2022.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here