Musulmai aka fi kashe wa a Najeriya ba kiristoci ba–AU

0
8

Shugaban Ƙungiyar Tarayyar Afirka (AU), Mahmoud Youssouf, ya bayyana cewa ba a kai hari ko kashe Kiristoci da gangan a arewacin Najeriya, kamar yadda ake yadawa a wasu kafafen yada labarai.

Youssouf ya yi magana ne a Ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya dake New York, inda ya ce rikicin tsaro a arewacin Najeriya ya fi rikitarwa fiye da yadda ake bayyanawa, kuma ba za a iya kiran sa “kisan kiyashin Kiristoci” ba.

Ya ce tun bayan bullar Boko Haram, Musulmai ne suka zama farkon mutanen da aka fi kashewa, sabanin ikirarin da wasu ke yi.

Ya kara da cewa AU ta yi nazari kuma ta bayyana a cikin sanarwar ta cewa babu wani irin kisan kiyashi na addini a arewacin Najeriya.

A kwanakin baya wasu manyan ‘yan siyasar Amurka da kafafen sada zumunta sun rika yadawa cewa ana kashe Kiristoci a Najeriya. Hakan ya sa wasu ‘yan majalisar dokokin Amurka suka bukaci daukar mataki kan Najeriya.

Shugaban Amurka Donald Trump ma ya zargi Najeriya da “cin zarafin Kiristoci”, yana kuma barazanar takaita taimakon Amurka ga kasar.

Sai dai gwamnatin Najeriya ta musanta wadannan zarge-zargen, yayin da Kungiyar Kiristoci ta CAN ke cewa har yanzu Kiristoci na fuskantar hare-hare a sassa daban-daban.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here