Wata babbar Kotun Tarayya ta bayar da umarni ga jam’iyyar adawa ta PDP ta bai wa tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido, damar tsayawa takarar shugabancin jam’iyyar.
Rahotanni sun nuna cewa mai shari’a Peter Odo Lifu ya bayyana cewa ba daidai ba ne matakin da PDP ta dauka na hana Lamido damar sayen fom din takarar.
Kotun ta kuma dakatar da gudanar da taron gangamin jam’iyyar na ranar Asabar, tana mai cewa an gaza wallafa jadawalin taron a kan lokaci kamar yadda dokar zaɓe ta bukata domin sanar da mambobin jam’iyyar.
Wannan umarni na baya-bayan nan shi ne na uku da ke takaita PDP daga ci gaba da shirye-shiryen taron da ake son gudanarwa domin zaben sabbin shugabanni a matakin ƙasa.
Sai dai jam’iyyar, karkashin jagorancin Umar Ilya Damagum, ta ce za ta ci gaba da shirye-shiryen taron saboda ita ma tana da wani umarnin kotu da ya ba ta damar cigaba da aiwatar da shirin.


