Zamu tsare mutuncin jami’an tsaro Masu masu aiki akan doka–Ministan tsaro

0
9

Ministan tsaro Mohammed Badaru, ya bayyana cewa gwamnati tare da rundunonin sojoji za su kare mutuncin duk wani jami’in tsaro da yake aiwatar da aikinsa bisa tanadin doka.

Badaru ya bayyana hakan ne yayin taron manema labarai na musamman daya gudanar a Abuja, wanda aka shirya domin bikin tunawa da sojojin da suka rasu wajen kare Najeriya.

Maganganun ministan sun biyo bayan takaddama da ta auku tsakanin Ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, da wani jami’in rundunar sojin ruwa kan wani filin da ake cece-kuce akan shi a Abuja, wanda ake zargin mallakin tsohon hafsan rundunar sojin ruwa, Vice Admiral Awwal Gambo ne.

Badaru ya ce, “A ma’aikatar tsaro da kuma dakarun mu, za mu ci gaba da kare duk wani jami’in da ke aikinsa bisa doka. Za mu tabbatar ba a cutar da shi ba muddin yana yin aikinsa yadda ya kamata.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here