Majalisar Tarayya ta amince da buƙatar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar ta neman amincewa ya aro Naira tiriliyan 1.15 domin cike gibi a kasafin kuɗin shekarar 2025.
A zaman da aka gudanar a ranar Laraba, majalisar dattawa da ta wakilai sun amince da bukatar ciyo bashin.
Tinubu ya bayyana cewa buƙatar ciyo bashin ta zama dole saboda faɗaɗa kasafin kuɗin daga adadin da aka fara tsara wa zuwa sama da abin da aka kiyasta a cikin kudaden shiga da kuma basussuka na cikin gida.
Kwamitin da Sanata Haruna Manu daga Taraba ta tsakiya ke wakilta ya ba da rahoton cewa ma’aikatar kuɗi da ofishin kula da bashi (DMO) sun tabbatar da cewa duk wani bashi an gudanar da shi cikin tsari mai gaskiya.
Sanata Abdul Ningi daga Bauchi ta tsakiya ya ƙara da cewa dole ne a tabbatar da cewa an yi amfani da kuɗin da aka aro a kan abubuwan da majalisa ta amince da su.


