An samu hannun jami’in gwamnatin Kano a satar motar ofishin mataimakin gwamna

0
9

Rundunar ‘yan sandan Jihar Kano ta bayyana cewa ta samu nasarar gano motar Toyota Hilux da aka sace daga ofishin mataimakin gwamnan jihar.

A cewar rahoton da ofishin mataimakin gwamnan ya samu daga ‘yan sanda, an gano motar ne da safiyar Laraba bayan bincike mai zurfi na hadin gwiwa tsakanin jami’an tsaro.

An kuma kama wanda ake zargi da satar motar, wanda aka bayyana cewa direba ne a gidan gwamnatin jihar. Yanzu haka yana hannun ‘yan sanda yana taimakawa wajen bincike.

Ofishin mataimakin gwamnan ya jinjinawa yadda rundunar ‘yan sanda ta gaggauta daukar mataki da kuma kwararrun hanyoyin da ta bi wajen gano motar.

A cikin wata sanarwa da sakataren yada labaran mataimakin gwamnan, Ibrahim Garba Shuaibu, ya fitar, ofishin ya bayyana cewa lamarin “cin amana ne daga direban da aka kama.”

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here