NSCDC ta kama ɓarayi da masu safarar miyagun ƙwayoyi a Kano

0
31

Hukumar tsaron a’lumma ta farin kaya NSCDC reshen Kano ta kama mutum biyu da ake zargi da aikata laifuka a karamar hukumar Kumbotso.

Jami’in hulɗa da jama’a na hukumar, Ibrahim Abdullahi, ya ce an kama wani matashi mai suna Usman Abdulhamid, mai shekaru 19 daga Yankanko, Panshekara, bayan da ya saci babur a yankin Sabuwar Jiddah. Ya kuma amsa cewa yana cikin wata ƙungiya da ke satar babura a sassan Kano. An kwato babura guda huɗu daga wurinsa, masu ƙirar Jincheng uku da Lifan ɗaya. Zuwa yanzu dai ana cigaba da nemo sauran abokan aikinsa biyu da suka tsere.

Haka kuma, hukumar ta kama wani da ake zargi da safarar miyagun ƙwayoyi, Salisu Abdullahi, mai shekaru 28 daga unguwar Samegu. An kama shi a Sabon Titin Dorayi dauke da kwalaye daban-daban na ƙwayoyi masu sa maye, ciki har da Paxol, Pregabalin, Diazepam, da wani maganin bugarwa na gajiya.

NSCDC ta ce waɗannan kamun na cikin kokarinta na daƙile masu aikata ɓarna da ke addabar al’umma. Yanzu haka ana ci gaba da bincike, kuma za a gurfanar da su kotu bayan kammala bincike.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here