Dakarun sojin Najeriya sun kai samame a yankin Faruruwa, kusa da kauyukan Goron Dutse da Tsaure a ƙaramar hukumar Shanono ta jihar Kano, inda suka halaka ‘yan bindiga da dama tare da kama wasu.
Rahotanni sun nuna cewa, a lokacin samamen, sojojin sun kwato babura kusan 30 da ‘yan ta’addan ke amfani da su wajen kai hare-hare a yankunan karkara.
Wannan samame, wanda ya kasance ɓangare na ci gaba da yaki da ‘yan bindiga a arewacin jihar Kano, ya haɗa da sintiri da kuma fatattakar mayakan da ke ɓoye a dazuzzuka.
Sai dai a yayin arangamar, an tabbatar da rasuwar soja ɗaya daga cikin dakarun da suka shiga aikin.
Shugaban ƙaramar hukumar Shanono, Hon. Abubakar Barau, ya yaba da jajircewar jami’an tsaro, tare da tabbatar da cewa za su ci gaba da basu goyon baya da duk wata taimako da suke buƙata.
Rahotanni sun ce an tura ƙarin dakarun ƙasa da na sama domin tabbatar da cewa ‘yan bindigar ba su sake samun damar komawa yankin ba.


