Shugaban Amurka Donald Trump ya umarci Ma’aikatar Yaƙin ƙasarsa da ta fara shirye-shiryen yiwuwar kai hari a Nijeriya, bisa zargin cewa ana yi wa Kiristoci kisan gilla a ƙasar.
A cikin wani saƙo da ya wallafa a dandalin Truth Social, Trump ya ce Amurka za ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Nijeriya idan gwamnatin ƙasar ta ci gaba da bari ana kashe Kiristoci.
> “Idan gwamnatin Nijeriya ta kasa kawo ƙarshen kisan Kiristoci, Amurka za ta shiga ƙasar da ƙarfin gwiwa domin kawar da ‘yan ta’adda masu tsaurin kishin Musulunci,” in ji Trump.
Trump ya kuma bayyana cewa ya umarci Ma’aikatar Yaƙi ta Amurka da ta shirya domin yiwuwar ɗaukar matakin soji, yana mai cewa harin zai kasance “mai sauri, da kaifi.”
Martanin Gwamnatin Nijeriya
A martanin da ya biyo bayan kalaman Trump, Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya jaddada cewa ƙasarsa tana nan daram a matsayin ƙasa mai mulkin dimokuraɗiyya da ke tabbatar da ‘yancin yin addini da haƙuri tsakanin mabambantan ra’ayoyi.
Tinubu ya ce tun bayan da gwamnatinsa ta hau mulki a 2023, tana gudanar da tattaunawa da shugabannin Kiristoci da Musulmai domin ƙarfafa haɗin kai da magance matsalolin tsaro.


