Rikicin jam’iyyar PDP ya ƙara kamari, yayin da wani sabon ɓangare daga cikin Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya sanar da dakatar da mukaddashin shugaban jam’iyyar, Ambasada Umar Damagum, da wasu manyan jami’an jam’iyyar guda biyar.
Wannan sabon ɓangare, wanda ake danganta shi da ministan babban birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, ya yi sanarwar ne a taron manema labarai da aka gudanar a Abuja ƙarƙashin jagorancin Sanata Samuel Anyanwu, wanda shi ne sakataren jam’iyyar na ƙasa.
A cewar Anyanwu, an nada Mohammed Abdulrahman, mataimakin shugaban jam’iyya na yankin Arewa ta Tsakiya, a matsayin sabon mukaddashin shugaban PDP.
Ya ce Damagum da wasu jami’an jam’iyyar sun yi sakacin aiki, cin hanci da saba wa hukuncin kotu, kuma an dakatar da su na tsawon wata ɗaya domin su gurfana gaban kwamitin ladabtarwa.
Sauran waɗanda aka dakatar sun haɗa da:
Debo Ologunagba, mai magana da yawun jam’iyya,
Taofeek Arapaja, mataimakin shugaban jam’iyya (Kudu),
Daniel Woyenguikoro, ma’ajin kuɗi na ƙasa,
Sulaiman Kadade, shugaban matasan jam’iyya, da
Setonji Koshoedo, mataimakin sakataren jam’iyya.
An ce za a gurfanar da su gaba ɗaya domin su bayyana dalilin da ya sa ba za a kori su daga jam’iyyar ba.
Sai dai a farkon ranar Asabar, ɓangaren da ke biyayya ga Damagum shi ya fara sanar da dakatar da Sanata Anyanwu da wasu uku daga cikin shugabannin jam’iyyar abin da ke nuna cewa jam’iyyar PDP ta rabu gida biyu a matakin shugabanci.


