Rikicin da jam’iyyar adawa ta PDP ke ciki ya sake daukar sabon salo a yau Asabar, bayan da aka dakatar da Sakataren jam’iyyar, Sanata Samuel Anyanwu, da wasu manyan jami’an jam’iyyar da ake ganin ‘yan bangaren Ministan Abuja, Nyesom Wike ne.
Mai magana da yawun jam’iyyar na kasa, Hon. Debo Ologunagba, ne ya sanar da dakatarwar bayan wani dogon taron da Kwamitin gudanarwa na jam’iyyar ya gudanar a hedikwatar PDP da ke Abuja.
Sauran wadanda abin ya shafa sun hada da Lauyan Jam’iyyat na Kasa, Kamaldeen Ajibade (SAN), Sakataren Shirye-shirye na Kasa, Umar Bature, da Mataimakin Lauyan Jam’iyya na Kasa.
Majiyar Daily Trust ta bayyana cewa wadanda aka dakatar sun dade ba sa halartar tarurrukan jam’iyyar. An dakatar da su na wata guda tare da tura batunsu zuwa kwamitin ladabtarwa.
Wannan na zuwa ne kwana guda bayan da wata kotun babbar birnin tarayya Abuja ta umarci PDP da ta dakatar da babban taronta na kasa da aka shirya gudanarwa a Ibadan a ranar 15 zuwa 16 ga Nuwamba, 2025.
Sai dai PDP ta ce za ta daukaka kara a kan hukuncin kotun, tare da bayyana cewa hakan ba zai hana ta ci gaba da shirye-shiryenta ba.
Rashin jituwa tsakanin mambobin jam’iyyar da bangarori masu adawa da juna ne ya janyo karar da aka shigar domin hana taron.


