NAHCON Ta Nuna Damuwa Kan Rashin Biyan Kuɗin Hajjin 2026

0
21

Hukumar Alhazai ta Kasa (NAHCON) ta bayyana damuwa kan jinkirin biyan kuɗin aikin Hajjin 2026 daga masu niyyar zuwa, lamarin da ka iya hana samun wuraren zama masu inganci a Makka da Madina.

Shugaban hukumar, Farfesa Abdullahi Saleh-Usman, ya ce hakan na iya jawo cikas wajen shirya aikin Hajji yadda ya dace. Ya bukaci goyon bayan gwamnonin Arewa maso Yamma wajen wayar da kan jama’a su biya kuɗin tun da wuri.

Saleh-Usman ya kuma jaddada irin tallafin da gwamnatin tarayya ta yi a shekarun baya, ciki har da Naira biliyan 90 da aka bayar a 2024 domin rage radadin hauhawar farashi, da kuma kudaden da aka biya kamfanonin jirgin sama na 2023.

Haka zalika, NAHCON ta dawo da Naira biliyan 5.3 ga jihohin da ba su samu hidimomin da aka biya su a 2023 ba, matakin da ya kara tabbatar da gaskiya da rikon amana a harkokin hajji.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here