Hukumar tace fina-finai ta jihar Kano ta fara kama matuƙa babura masu liƙa hotunan Batsa

0
48

Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta Jahar Kano ta fara kamen matuka babura masu kafa uku da ke lika hotunan batsa tare da kalaman da basu dace ba.

Bayanin hakan na cikin wata sanarwa daga Abdullahi Sani Sulaiman Jami’in yada labarai na Hukumar tace fina-finai da Dab’i ta Jahar Kano.

Tuni shugaban Hukumar Abba El-mustapha ya aike da jami’ansa kan manyan titinan Jahar Kano domin sa ido ga matuka babura masu kafa uku tare da kama duk wani babur da aka samu sanye da hotunan batsa ko rubuta kalaman da basu yi daidai da tarbiya ba.

Abba El-mustapha yace wannan na daga cikin ayyukan da ya rataya a wuyan Hukumar na tabbatar da anyi hoto mai tsafta tare da lika shi a inda ya dace, haka kuma, na daga cikin aikin Hukumar ta tantance duk wani rubutu kafin ya isa ga idanun a’lummar Jahar Kano.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here