NLC ta saka ranar fara yajin aiki a jihohin da suka ki biyan mafi karancin albashi

0
63
NLC
NLC

Kungiyar kwadago ta kasa NLC ta umarci yayan ta su fara yajin aikin sai baba ta gani daga ranar 1 ga watan Disamba na shekarar 2024, a jihohin da suka ki fara biyan mafi karancin albashin ma’aikata na naira dubu 70.

Umarnin, ya biyo bayan gudanar da taron kungiyar kwadago na kasa daya gudana a birnin Fatakwal dake jihar Rivers, inda aka jiyo shugaban kungiyar NLC na kasa Joe Ajaero, na nuna takaicin sa akan yadda al’umma ke cigaba da fuskantar tsadar rayuwa a Nigeria, da tabarbarewar tattalin arziki.

Ajaero, yace cin amana ne wasu gwamnonin suke aiwatar wa wajen kin amincewa da dokar biyan sabon mafi karancin albashin ma’aikata.Haka zalika, NLC tace ana take hakkin ma’aikata da kin biyan su abin da ya dace.

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here