HomeLocal NewsAn maka Gwanja, Safara’u, 442 da wasu ƴan TikTok a kotun Shari’ar...

An maka Gwanja, Safara’u, 442 da wasu ƴan TikTok a kotun Shari’ar Muslunci a Kano

Date:

Related stories

Emir of Daura backs Tinubu’s re-election bid

The Emir of Daura, Alhaji Umar Faruq, has thrown...

Kano launches ‘Safe Corridor’ to combat youth crime, insecurity

The Kano State Government has reaffirmed its commitment to...

Kano govt to upgrade Dabai Hospital, extend working hours

In a move to improve access to emergency healthcare,...

UN applauds Gov Yusuf’s social, climate initiatives in Kano

Kano State Governor Abba Kabir Yusuf has earned praise...

Police arrest serial phone thief in Kano

The Kano State Police Command has apprehended a 27-year-old...
spot_img

An maka shahararrun mawaƙan zamani na Arewa da fitattun jaruman TikTok a gaban Babbar Kotun Shari’ar Musulunci da ke yankin Bichi a Kano bisa zargin rashin tarbiyya.

Duk da cewa DAILY NIGERIAN ba ta samu kwafin ƙarar ba, amma majiyoyi sun ce laifuffukan sun haɗa da wakokin rashin tarbiyya da rawar Tiktok da ke da alaƙa da lalata tarbiyyar al’umma.

Sai dai jaridar ta samu kwafin wasikar da kotun shari’ar Musulunci ta rubuta wa ƴan sanda na neman a binciki koke-koken da ke gaban masu gabatar da ƙara.

Wadanda aka zayyana a wasikar da aka aika wa kwamishinan ‘yan sandan jihar Kano sun hada da 442, Safara’u, Dan Maraya, Amude Booth, Kawu Dan Sarki, Ado Gwanja, Murja Kunya, Ummi Shakira, Samha Inuwa da Babiyana.

“Sakamakon karar da Muhd ​​Ali Hamza Esq, Abba Mahmud, Esq, Sunusi I. Umar Esq, Abba, A.T Bebeji Esq, B.I Usman Esq, Muhd ​​Nasir Esq, L.T Dayi Esq, G.A Badawi & Badamasi Suleiman Gandu Esq su ka gabatar.

“Alkali mai shari’a na Babbar Kotun Shari’a na Bichi a Kano ya umurce ni da in rubuta tare da neman ku da ku gudanar da bincike a kan wadanda ake zargin a sama domin daukar matakin da ya dace.

“An maƙala kwafin takardar korafin don ƙarin bayani. Ka huta lafiya,” in ji wasiƙar, wacce rijistaran kotun, Aminu Muhd ​​ya sanya wa hannu.

 

DAILY NIGERIAN

Subscribe

Latest stories

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here