HomeLocal NewsAFDB ya ware Dala biliyan daya da rabi domin shawo kan matsalar...

AFDB ya ware Dala biliyan daya da rabi domin shawo kan matsalar karancin abinci

Date:

Related stories

KASUPDA urges Rigasa residents to secure building permits for safer communities

The Kaduna State Urban Planning and Development Authority (KASUPDA)...

Kano Anti-Corruption Commission seizes over 1,000 plots of land

The Kano State Public Complaints and Anti-Corruption Commission has...

Kano: Residents warned as bird flu kills 37 chickens in Gwale

Dr. Abdullahi Abubakar Gaya, Chief Medical Officer of Gwale...
spot_img

Bankin raya kasashen Afrika na AFDB ya amince da ware Dala biliyan daya da rabi a matsayin agajin gaggawa domin taimakawa jama’ar dake nahiyar wajen shawo kan matsalar karancin abinci sakamakon yakin kasar Ukraine.

Shugaban Bankin Akinwumi Adeshina ne ya sanar da daukar matakin inda yake cewa za’a yi amfani da kudaden ne wajen taimakawa kasashen dake nahiyar wajen samar da abincin da ake bukata.

Adeshina yace akalla manoma miliyan 20 dake Afirka zasu amfana daga wannan shiri domin noma tan miliyan 30 na nau’in abinci iri iri da suka hada da alkama da masara da waken soya wadanda ake sayowa daga Ukraine.

‘Ƴan Najeriya sun kashe fiye da naira biliyan 100 wajen neman ilimi a ƙasashen ketare cikin wata uku

Shugaban bankin yace a karkashin wannan shirin ana bukatar noma tan miliyan 38 na abincin da ya kunshi tan miliyan 11 na alkama da tan miliyan 18 na masara da tan miliyan 6 na shinkafa da kuma tan miliyan biyu da rabi na waken soya.

Subscribe

Latest stories